ABNA24 : A zanatawar da ya yi da takwaransa na kasar Japan a daren jiya ta hanyar wayar tarho, ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, Japan kasa ce da take da kyakkayawar alaka da kasar Iran tsawon tarihi, saboda haka bai kamata ta bari Amurka ta ta kawo matsala a cikin wannan tsohowar alaka ba.
Ya ce biliyoyin daloli mallakin kasar Iran da suke a cikin bankunan kasar Japan, wanda gwamnatin kasar Japan ta kasa fitar da su domin mika su ga kasar ta Iran, domin tsoron takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran.
A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Japan ya tabbatarwa Zarif da cewa, suna daukar matakan da suka dace domin ganin cewa Iran ta karbi hakkokinta da ke hannun kasar Japan, kuma kasashen biyu za su ci gaba da kara bunkasa alakarsu a dukkanin bangarori.
342/